Home » Kamfanin Adobe sun sayi Figma

Kamfanin Adobe sun sayi Figma

Figma manhajar da ake amfani dashi wajen tsara UI/UX Wanda shine mafi shahara manhajar kirkirar UI/ UX sun fitar da sanarwar da ke nuna sun sayar da kamfanin nasu ga Adobe akan kuɗi dalar Amurka biliyan 20.

Adobe babba kamfani da suka kasance a sahun gaba wajen samar da manhajar design da kuma editing, suna kuma da manhajar da ake amfani dashi wajen yin UI/UX din suma,amma sun yanke shawarar sayan Figma a farashi mai yawa.

Masu fashin baki na ganin Adobe sun sayi Figma ne kasancewar itace kawai abokiyan hamayya Adobe a abinda ya shafi kirkirar design na UI/UX, inda a yanzu da suka saya ya zama babu wani baraza da suke fiskanta a tsarin kasuwanci su, sakamakon saye abokin karawar nasu.

Designers da dama sun nuna rashin jin dadin su akan faruwar hakan, inda suke tunani Adobe zasu iya kara kudi fiye da kima na amfani da Figma,sai dai CEO kamfanin na Figma ya tabbatar da cewa komai zai kasance a yanda yake, kuma shine ma zai cigaba da jagoranta kamfanin na Figma dake ƙarƙashin Adobe a yanzu.

Related Posts