Home » Rashin kudin gudanarwa ya sa mai kamfanin Lazerpay rufe kamfanin 

Rashin kudin gudanarwa ya sa mai kamfanin Lazerpay rufe kamfanin 

Kamfanin crypto da web3 na Najeriya, Lazerpay ya rufe ayyukansa, biyo bayan gazawar sa na samun karin kudade daga masu zuba hannun jari.

Tun a kwanakin baya kamfanin ta fara korafin rashin kudin gudanarwa, wanda har ya kaisu ga sallamar ma`aikatan su  da dama a wanchan lokaci.sai dai duk da wannan bai saka kamfanin ta iya cigaba da gudana yanda ya dace ba.

Njoku Emmanuel

Njoku Emmanuel matashin da ya samar da kamfanin yana da shekara 19 a lokacin da ya ƙirƙiro Lazerpay a 2021. Shine  kuma ya cigaba da kula da kamfanin tare da taimakon sauran ma`aikata da yake aiki dasu,har zuwa wannan lokaci daya fitar da wannan sanrwa inda yake cewa.

sanarwan da ya wallafa

“Duk da kokarin da kungiyar mu ta yi na samar da kudaden da ake bukata don ci gaba da Lazerpay, ba mu samu nasarar tara kudade ba.” “Mun yi gwagwarmaya sosai don ci gaba da kula da wannan kamfanin tsawon lokacin da zai yiwu, abin takaici, yanzu muna kan matakin da ya kamata mu rufe.”

Related Posts