Home » Moniepoint sun musanta maganar dake yawo cewa sun sayi PayDay 

Moniepoint sun musanta maganar dake yawo cewa sun sayi PayDay 

Moniepoint, wani bankin kasuwanci a Najeriya,sun musanta rahotannin dake nuna cewa sun sayi kamfanin PayDay. Wannan na zuwa ne bayan WeeTracker, wata mujallar fasaha ta Afirka, ta ba da rahoton cewa Moniepoint na shirin siyan PayDay akan dala miliyan 40 bayan ta jagoranci Pre-seed da PayDay sukayi na dala miliyan 3.

A cewar WeeTracker, Moniepoint da PayDay suna tattaunawa domin ganin Moniepoint ta mallaki PayDay, kusan watanni uku kenan ana tattaunawa. Jaridar ta kuma yi iƙirarin cewa adadin kudin da moniepoint ke shirin biya yakai kimanin dala miliyan 40. Amma Moniepoint sun musanta rahotannin, tare da bayyana cewa Moniepoint ta saka hannun jari ne kawai a PayDay.

Duk da wannan musantawa, wasu majiyoyi sun ce yarjejeniyar tana kan tebur kuma mai yiwuwa har yanzu za ta ci gaba cikin watanni uku. Sun yi iƙirarin cewa an cimma yarjejeniya bisa ƙa’ida kuma ba zai zama abin mamaki ba idan yarjejeniyar ta gudana kamar yadda ake tunanin sayan yana da ma’ana ga Moniepoint. A cewar TechCrunch, a baya PayDay ya ki amincewa da tayin sayan dala miliyan 15 daga wani Babban Kamfani a Afirka.

Related Posts