Home » Rijistar NIN: Shafin Hukumar NIMC Ya Samu Matsala

Rijistar NIN: Shafin Hukumar NIMC Ya Samu Matsala

A daidai lokacin da ‘yan Nijeriya suke fafutikar ganin sun yi rijistar lambar NIN ta katin dan kasa, wacce ake hadawa da layin wayar salula; shafin hukumar NIMC na yin rijistar ya samu matsala inda masu kokarin yin rijistar suke kasa bude shafin ma gaba daya. Sakamakon yawa da mutane suka yi wajen ganin sun bude shafin don yi rijista kafin wa’adi mako biyu da gwamnatin tarayya ta sanya.
Mafi yawan korafin ana yin shi ne a shafin Twitter inda ake jawo hankalin ministan sadarwa da kuma shugaban hukumar kan matsalar da shafin ya samu, mafi yawan ‘yan Nijeriya basu da lambar NIN da ake bukatar a hada da layukan wayoyin sadarwa, wanda a cewar ministan sadarwa duk wanda bai hada layinshi da lambar ta NIN ba, toh hukumar ta umarci kamfanonin sadarwa da su rufe layin.
Matsalar ta fara ne tun misalin karfe 3:30 na yammacin yau Litinin, daga cikin masu korafin harda wadanda suke bukatar ministan sadarwan da ya gaggauta yin murabus, saboda a cewarsu wannan gazawar daga gareshi take.