Home » Za’a rufe rufe duk wani layin waya da ba a yi wa rajista da lambar shaidar zama ɗan ƙasa ta NIN ba

Za’a rufe rufe duk wani layin waya da ba a yi wa rajista da lambar shaidar zama ɗan ƙasa ta NIN ba

Hukumar da ke kula da harkokin sadarwa ta Najeriya wato NCC ta bayar da umarnin rufe duk wani layin waya da ba a yi wa rajista da lambar shaidar zama ɗan ƙasa ta NIN ba ko da kuwa layin tsoho ne.
Hukumar ta bayar da wa’adin makonni biyu ga masu layin waya waɗanda ke da wannan lambar ta NIN da su kai ta ga kamfanonin sadarwar da suke da rajista da su domin a sabonta musu rajistar lambar da layin wayarsu.
Wannan na zuwa ne bayan hukumar ta bayar da umarnin a dakatar da sayarwa ko rajistar sabbin layin waya a ƙasar.
Mutum zai iya duba lambarsa ta NIN ta hanyar latsa wadan nan lambobi *346# zakayi amfani ne da layin da kayi rijista shaidar kasa dashi domin dubawa.
Lambobi zasuyi amfani a kowani layin waya da mutum yake aiki dashi MTN, AIRTEL,Glo da Kuma 9mobile za’a cire kudi naira 20 a layin naka kamin ka samu ganin NIN number Ka.