Home » Yanzu za ku iya gyara kuskuren da kuka yi a saƙon Whatsapp da kuka tura

Yanzu za ku iya gyara kuskuren da kuka yi a saƙon Whatsapp da kuka tura

Kamfanin da ya mallaki manhajar Whatsapp ya ce yanzu mutane za su iya gyara kuskuren da suka a saƙon da suka tura, kamar yadda akan iya yi a wasu mahajojin irin su Telegram da Signal.


Kamfanin ya ce za a iya gyara kuskuren da aka yin ne a cikin minti 15 bayan tura saƙon.
Whatsapp manhaja ce mallakar kamfanin Meta na murka, wanda shi ne ya mallaki Facebook da Instagram.A cikin makonni masu zuwa ne za a samar da tsarin iya gyara kura-kuren ga mutane biliyan biyu da ke amfani da Whatsapp a faɗin duniya.

Masu manhajar sun ce “Za a iya gyara kuskuren da aka yi wajen rubutu ko a yi ƙarin bayani a kan saƙon, wannan wata dama ce da za ta ba ku ikon sarrafa saƙonninku yadda kuke so.”Saƙon ya ƙara da cewa hanyar da za a bi wajen gyara kuskuren ita ce “A danna kan saƙon na tsawon daƙiƙu, sai a zaɓi ‘Edit’ daga cikin saƙon da zai fito, ana iya yin haka a cikin minti 15 bayan tura saƙo.”
Sai dai za a nuna wa wanda aka tura wa chat ɗin cewa an yi gyara a saƙon.Amma ba za a nuna masa tsohon bayanin ba.

Related Posts