Home » Zainnest yayi nasarar samun gurbi a AWS Africa Fintech Accelerator 

Zainnest yayi nasarar samun gurbi a AWS Africa Fintech Accelerator 

Zainnest na daya daga cikin Startup da sukayi nasara shiga AWS Africa Fintech,shiri na musamman da kamfanin na Amazon suka samar domin tallafawa tare da bada horo na tsawon sati goma ga startup da suka shafi fintech.

Startup Ashirin da hudu 24 ne aka tantance za`a musu horon a Afrika goma sha daya 11 daga ciki startup ne da suke Nijeriya, Zainnest Startup da matashi daga Arewacin Nijeriya ya kirkira, yana daya daga cikin 11 da aka zaba.

Zainnest manhaja ce da ake iya tura kudi,sayan katin waya, sayan Data,yin Tv subscription da duk sauran abubuwan da ake biyan kudin su ta hanyar yanar gizo,manhajar nada saurin aiki da kuma biyan bukata, domin fara amfani da zainnest sai ku ziyarci wannan adreshin.  

Related Posts