Home » AKAN BATUN REJISTAR KAMFANI (C.A.C) KYAUTA.

AKAN BATUN REJISTAR KAMFANI (C.A.C) KYAUTA.

Gwamnatin Buhari ta amince a yi wa ƙananan ƴan kasuwa rijistar kamfani kyauta. Gwamnatin Najeriya ta fara yi wa mutane rijistar kamfani kyauta domin samun tallafin rage raɗaɗin da suka samu kansu a ciki sakamakon annobar cutar korona.
Tallafin na gwamnatin tarayya ya shafi bai wa ƙananan ƴan kasuwa jarin naira 250,000 domin damar yin rijistar kasuwancinsu.
A ranar Litinin hukumar CAC da ke kula da rijistar kamfanoni ta fara aikin yi wa mutane rijistar kamfani kyauta, kuma hukumar ta bayyana a shafinta na intanet cewa jami’anta za su shafe tsawon wata uku suna aikin rjistar.
Gwamnati ta ce dole kafin mutum ya samu tallafin wanda aka ware naira biliyan 75 domin farfaɗowa da bunƙasa masu kanana da matsakaitan masana’antu a Najeriya, dole sai yana da kamfani.
Hukumar CAC ta ce gwamnatin Najeriya ta amince a yi wa mutane rijistar kamfani kyauta a jihohin ƙasar 36 haɗi da Abuja.
Ga abubuwa da suka kamata ku sani game da tsarin gwamnati na yi wa mutane rijistar kamfani kyauta:
Adadi
Gwamnatin tarayya ta amince a yi wa mutum 6,606 rijistar kamfani kyauta a jihohi 34 na ƙasar.
Amma a Kano adadin mutum 8,406gwamnati ta amince a yi wa rijistar kamfani kyauta, jihar Legas kuma mutum 9,084, sai jihar Abia mutum 7,906.
Gwamnantin ta ce wannan dama ce ga dukkanin masu sha’awar yi wa kasuwancinsu rijista musamman masu sana’o’in hannu domin inganta kasuwancinsu a hanyoyin da suka kamata.
Cancanta
Hukumar CAC ta ce kowa yana da damar zuwa a yi masa rijistar kamfaninsa a kyauta
Amma tsarin kuma ya shafi gwamnatocin jihohi da za su gabatar da sunayen wadanda suke so a yi masu rijista.
Mutum ɗaya ko biyu suna iya rijistar kamfani na haɗin guiwa tsakaninsu.
Abubuwan da ake buƙata.
Ana buƙatar mutum ya zabi sunaye uku ga wanda ke son yin rijistar kamfaninsa
A ciki za a zaɓi suna ɗaya amma sai idan ya kasance babu wanda ke amfani da sunan a matsayin kamfani.
Ana buƙatar adreshi na gida ko na kamfani
Mutum zai faɗi irin kasuwancin da yake so ya yi kamar tela ko kanikanci ko duk irin sana’ar da yake yi.
Ana buƙatar hoto guda biyu da lambar waya da kuma adireshin imel idan mutum yana da shi.
Ana kuma buƙatar katin sheda, kamar katin ɗan ƙasa ko na lasisin tuƙi ko fasfo ko kuma katin zaɓe.
Ina ake rijistar?
Hukumar CAC ta ware cibiyoyin yin rijistar a dukkanin jihohi, kuma za a iya ziyartar reshenta na jihohi.
Hukumar ta kuma wallafa sunayen jami’anta da ke jagorantar aikin rijistar a dukkanin jihohi da lambobinsu na salula da za a iya tuntuba, wanda za ku iya samu idan kuka danna nan
Za a ci gaba da rijistar har zuwa watan Disamban shekarar nan.
BBC Hausa