Home » Za a rage kudin data a Najeriya

Za a rage kudin data a Najeriya

Ma’aikatar sadarwa ta Najeriya ta ce ta fara shiri na rage kudin data da ake amfani da ita wajen shiga intanet a kasar.
Shugaban Hukumar Sadarwa ta Najeriya wato NCC Farfesa Umar Danbatta ne ya bayyana hakan a zantawarsa da maneema labarai, inda ya ce gwamnati na son mayar da kudin data din zuwa naira 390 kan ko kowane gig guda.
Farfesa Danbatta ya ce gwamnatin kasar na son fara aiki da wannan sabon farashin na data nan da shekaru 3 zuwa 5 kuma kafin yin hakan za a samar da irin tsarin na bada intanet mai karfi wato broadband a mafi akasarin kasar.