Home » WhatsApp za a fitarda sabon tsarin da zai bada daman batar da sako bayan kwana bakwai.

WhatsApp za a fitarda sabon tsarin da zai bada daman batar da sako bayan kwana bakwai.

Manhajar Whatsapp za ta fito da wani sabon tsari na bai wa masu amfani da manhajar damar ɓatar da saƙonnin da aka turo musu ko kuma suka tura bayan mako guda.
Manhajar ta Whatsapp, wadda mallakar shafin Facebook ce, na da mutane masu amfani da ita biliyan biyu a faɗin duniya, haka kuma kamfanin ya ce wannan matakin zai taimaka wajen sirrinta saƙonnin da aka aika.
Sai dai manhajar ta ce waɗanda aka aika wa saƙon za su iya su ɗauki hoton saƙon da aka turo musu ko kuma sake aika saƙon ko hoto ko bidiyon da ba sa so manhajar ta goge.
Ana sa ran zuwa ƙarshen watan Nuwamba ne masu amfani da manhajar ta Whatsapp za su fara amfani da wannan tsarin.
A wani shafi na intanet, kamfanin ya bayyana cewa mutum zai iya sakawa bayan mako guda saƙonnin wayarsa su ɓace, domin bai wa mutum sanyin zuciya na cewa saƙonnin ba za su zauna din-din-din ba.
A watan Afrilun 2019, shugaban kamfanin Facebook, Mark Zuckerberg ya yi alƙwarin yin sauye-sauye da dama ga tsarin shafin domin bai wa masu amfani da shafin tabbacin sirri.
Kamfanin kuma na so ya gwamutse wasu daga cikin manhajojin aika saƙon, inda za a game Whatsapp da Instagram da Facebook Messenger su zama suna iya musayar bayanai.
Manhajar Snapchat, wadda takwararsu ce daga wani kamfani daban, na da irin wannan tsarin na ɓacewar saƙonni bayan wani ɗan lokaci.