Home » Google ya bude damar samun naira miliyan 75 ga ƙananan ƴan kasuwa a Nijeriya

Google ya bude damar samun naira miliyan 75 ga ƙananan ƴan kasuwa a Nijeriya

A ranar Alhamis ne Google ta yi kira ga kanana da matsakaitan ‘yan kasuwan Nijeriya da su nemi damar samun naira miliyan 75 na Asusun ‘Hustle Academy’ da aka bude.

Wannan asusun a cewar Google an bude shi ne domin bayar da kudin kyauta ga kananan ‘yan kasuwa da matsakaitan da suka cancanta.

Shugaba kuma jagorar kyautata alaka na Kamfanin na Google wacce ita take Yammacin Afrika, Mojolaoluwa Aderemi-Makinde ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa inda ta ce shirin zai bayar da Naira miliyan 5 ga masu kanana da matsakaitan sana’o’i goma sha biyar a Nijeriya.Aderemi-Makinde ta ce, wannan shiri ya kara tabbatar da irin kwazon da Google take da shi wajen bunkasa harkokin kasuwanci a Nijeriya.

Ta kuma kara da cewa masu kanana da matsakaitan sana’o’i a Nijeriya sune kashin bayan tattalin arzikin Nijeriya amma suna fama da kalubale, musamman ta fuskancin hanyar samun kudade.Aderemi-Makinde har wala yau ta kara da cewa bankin duniya ta ce kananan sana’o’i da matsakaita a Afirka na fuskantar gibin kudi har na dala biliyan 330.

Ta kuma ce, kashi 25 ne cikin 100 kacal na masu kanana da matsakaitan sana’o’i ne kawai a Afirka ne ke samun lamuni a banki, adadin da ya sha bamban da kashi 50 da ake so cikin 100 a kasashe masu tasowa.

“Asusun Hustle Academy wata shaida ce da take nuna juriya da kirkire-kirkire na kananan ‘yan kasuwan Nijeriya, wadanda su ne kashin bayan tattalin arzikinmu.“Muna fatan wannan asusu zai kara basu karfin gwiwa wajen samun nasara da bunkasar tattalin arziki, samar da ayyukan yi da dama ga daukacin ‘yan Nijeriya,” in ji ta.

Aderemi-Makinde

A cewarta, shirin ‘Google’s Hustle Academy’, an soma gabatar da shi a cikin 2022, inda yake bai wa masu kanana da matsakaitan sana’o’i ilimin kasuwanci da na gudanarwa, jagoranci, da kuma hanyar sadarwa, tare da nuna musu hanyar da za su rika bunkasa kasuwancin su.

Aderemi-Makinde ta ce, ana yin hakan ne domin a samar da jarin da ya kamata domin bunkasa sana’o’insu zuwa gaba.Ta ce tun lokacin da aka fara shirin, shirin ya yaye sama da sana’o’i 4,000 a Nijeriya, wanda kashi 74 cikin 100 na rahoton shekarar farko ya nuna ci gaban kasuwanci.

A cewarta, wadanda za su ci gajiyar shirin na asusun dole ne ya zama dan Nijeriya wanda ya samar da kasuwancinsa a kasar kuma yana gudanar da kasuwancin tsawon shekaru 1 zuwa 5, kuma ya kasance suna da tsarin kasuwanci mai tsafta.Ta ce ya kamata kasuwancin ya kasance yana da tarihin sadaukar da kai domin ci gaba, tare da gudanar da aikinsa a bangaren da suka dace da tattalin arzikin dijital ko kuma suna da dabarun ba da damar ayyukan dijital.Ta ce za a bude wannan damar ne daga ranar Talata 3 ga Oktoba a kuma rufe a ranar 12 ga watan Oktoban 2023.

Related Posts