Home » Amfanin Katin Zare Kudi Na ‘Master Card’ Guda Shida Da Ba Ku Sani Ba

Amfanin Katin Zare Kudi Na ‘Master Card’ Guda Shida Da Ba Ku Sani Ba

Katin zare kudi (Debit Card), kamar yadda muka sani, ana amfani da shi sosai a tsakanin masu amfani da asusun banki a fadin duniya Katin ya kawar da buƙatar ɗaukar tsabar kuɗi a hannu ana yawo da shi a ko’ina da za a shiga. Ba wai kawai suna saukaka mu’amala ta kuɗi bane daƙiƙa kaɗan, a’a amma yarda da shi sosai a fadin duniya.

Tun kama daga mai sayar da kayan abinci na gida zuwa manyan gidajen cin abinci da kantuna, za ku iya amfani da katin zare kudinku wanda ke da alaƙa da asusun bankin ku wajen biyan abin da kuka saya.

Da yawan mutanenmu ba su san bambance-bambancen dake tsakanin katinan zare kudi (ATM) da ake da su shahararru guda uku ba musamman wadanda ake cire kudi da su wato ‘Debit Card’ a turance.

Akwai katuna har guda uku shahararru da ya hada da ‘Verve Card’, sai ‘Visa Card’ sai kuma ‘Master Card’. Sai dai a wannan makala ba bayani za mu gabatar ba a kan bambance-bambancen dake tsakaninsu ba, a’a za mu yi bayani ne dangane da amfanin da ‘Master Card’ ke da shi.

Shafin TECH HAUSA ya yi bincike domin wayar da kan al’umma dangane da wannan katin da irin alfanunsa ga masu amfani da shi.

Ga wasu kadan daga cikin amfaninsa guda shida (6):

  1. Saukin amfani da shi

Katin zare kudi na ‘Master Card’ yana da matukar sauƙin amfani. Tunda ana cire kuɗin ne kai tsaye daga asusun bankin ku, inda kake tanadin kuɗinka, ana iya cire kudin nan take ba tare da wata matsala ba. Yana da saurin gaske fiye da ka jira sai ka ji shigar kudi wanda hakan ka iya haifar maka da damuwa ko fargabar karancin kudi a hannunka. Katin zare kudin yana da saurin mu’amala, sannan yana da sauƙi da kuma dacewa wajen amfani da shi.

  1. Yana biyan bukata da gaggawa

Katin zare kudin yana da ikon ba ku damar cirar tsabar kuɗi. Yana aiki fiye da daya domin a lokacin guda za ku iya amfani da na’urar ATM wajen cirar kudinku dake asusun bankinku a kowanne banki da kuka so. A don haka zai iya biyan bukatarka da gaggawa a lokacin da kake son cirar kudi a na’urar ATM. Akwai shagunan da suke biyan ku wani lada idan kuka sayayya da su ta hanyar amfani da ‘Master Debit Card’ dinku. Sannan za ka iya cinikayya da shi a koyaushe ba tare da wani fargaba ba.

  1. Yana da tsaro sosai

Ana kiyaye katin zare kudin da lambar sirri (PIN) guda hudu wacce za ka saita ta da kanka. Wannan lambar sirri yana da muhimmancin gaske a yayin aikata kusan kowane cinikayya ko sayayya ta hanyar amfani da katin. Sannan wannan lambar sirri zai ba ku babban kariya daga sata ko ‘yan dandatsa. Haka nan za ku rika karɓar sanarwa a duk lokacin da ka yi cinikayya domin tabbatar da cewa kai ne. Sannan ana iya daskarar da katin nan take cikin sauƙi kuma da sauri. A don haka idan ka rasa shi, za ka iya lalata shi ta hanyar daskarar da shi cikin ɗan karamin lokaci.

  1. Yana da sauƙin samu

Abu mafi mafi muhimmanci da dole kake da bukata ya zama ka samu wannan katin domin ka rika zare kudinka shi ne asusun banki. Kowa na iya bude asusun banki tare da mafi karancin kudin ajiya. A yau ma wasu bankunan a kyauta ake bude su. A don haka, za ku iya amfani da katin zare kudi tare da aka hada shi da asusun bankinku.

  1. Saita kasafin kudi

Ɗaya daga cikin abubuwan mafi kyau dangane da wannan katin na zare kudi na ‘Master Card’ shi ne ba za ku iya kashe kuɗi fiye da wanda kuke da shi ba, wanda hakan ke nufin ba za ku fada cikin bashi ba. Wannan zai taimaka maka wajen tsara kasafin kashe kuɗi, tunda duk lokacin da kuka yi mu’amala da katin, ana cire kuɗin ne daga asusunku.

  1. Biyan kudi ta hanyar Intanet cikin sauki

A yau akwai shafukan Intanet da dama na saye da sayarwa da za ka iya amfani da wannan katin kadai wajen biyan abubuwan da ka saya daga gare su. Wanda da yawan lokuta idan ba da wannan katin ba, to sam ba za ka iya biyan kudaden kayanka da ka saya daga gare su ba. Kazalika akwai shafukan sada zumunta da dama wanda da wannan katin kadai ne za ka iya biyan kudaden talla da kake son a tallata maka na kasuwancinka ko hajarka domin samun karin kwastamomi.

Wadannan sune amfani guda shida (6) da wannan katin cire kudi na ‘Master Card’ ke da shi ga duk wanda yake mu’amala da banki a yau. Kuma a mafi yawan bankunan Nijeriya cikin sauki za ka same shi idan kana da bukata kuma a nan take.

Related Posts