Home » Yadda nake son kawo sauyi a bangaren sadarwa a Nijeriya cikin shekaru 4 –Ministan Sadarwa

Yadda nake son kawo sauyi a bangaren sadarwa a Nijeriya cikin shekaru 4 –Ministan Sadarwa

Bosun Tijani, ministan sadarwa, kirkire-kirkire, da tattalin arzikin zamani (dijital) na Tarayyar Nijeriya, ya kaddamar da daftarin tsarin dabarun ma’aikatar sadarwa, kirkire-kirkire da tattalin arziki na zamani.

Daftarin wani gagarumin yunkuri ne na bunkasa bangaren tattalin arzikin zamani na Nijeriya daidai da manufar farfado da fata ga ‘yan Nijeriya na Shugaban Bola Ahmed Tinubu.

Daftarin kudurorin wanda aka yi wa take da “Haɓakar ci gabanmu ta hanyar Fasaha”, ba rubutun takarda ce kawai ba; a’a yana wakiltar tsarin canjin yanayin yadda Nijeriya za ta tunkari bangaren kirkire-kirkire da fasaha.

Wannan daftarin ya samo asali ta fuskacin gudanar da ayyuka a bude, samun haɗin kai, sannan har wala yau wannan tsarin daftarin da aka fitar sakamako ne na tattaunawa mai zurfi tare da masu ruwa da tsaki daban-daban a cikin ma’aikatar, abokan hulɗar kasuwanci, ƙungiyoyi masu sadaukarwa, wanda hakan ke nuna karfin da haɗin gwiwa mai muhimmanci ke da shi.

A jigon sa, daftarin ya yi hasashen Nijeriya a matsayin wacce za ta bunƙasa bangaren tattalin arzikin zamani, tare da samar da yanayi wanda ayyukan ƙirƙira da fasaha zai haifar da kawo tsari mai kyau ta fuskacin bunkasa tattalin arzikin zamani tare da haɗa kai. Daftari ne mai dauke da hangen nesa, wanda ke nufin ba kawai sanarwa aka yi da shi ba, har ma domin sake fasalin tsarin al’umma, samar musu da daidaito, bunkasa gaskiya da kuma rikon amana a tsakaninsu a yayin gudanar da ayyukansu.

Shirin daftarin na shekaru hudu daga 2023-2027 ya zayyana ginshiƙai guda biyar waɗanda suka zama tushen wannan tafiya ta kawo canji:

Ƙarƙashin ginshiƙi na farko, tsarin daftarin na neman sauya Nijeriya zuwa cibiyar fasaha ta duniya. Wannan manufar ta samo asali ne ta hanyar yunƙuri domin haɓaka ilimin dijital, zurfafa haɗin gwiwar bincike na duniya, tare da kuma sanya Nijeriya a matsayin babbar cibiyar ƙwararrun fasaha da babu kamar ta.

Rukuni na biyu ya jaddada muhimmiyar rawar da kyawawan tsare-tsare da manufofi ke takawa wajen rayar da kirkire-kirkire da kuma ayyukan kasuwanci. Wanda daftarin ya ce idan aka tsara manufofin da ke cike da hankali hakan zai sanya su jawo mutane masu hazaka tare da saka hannun jari, tare da samar da fage mai kyau ga tsarin ƙirƙira a Nijeriya domin bunƙasawa tare da tabbatar da samun dama dangane da fa’idodin dake cikin tattalin arzikin dijital.

Rukuni na uku ya mai da hankali ne dangane da ƙarfafa kayayyakin ayyukan dijital. Tare da haɗin da yake akwai tsakanin ingantattun tushe na wannan bangare da kuma wadatar tattalin arziƙi, wannan tsarin ya ba da fifikon faɗaɗa hanyar yanar gizo, inganta hanyar sarrafa yanar gizo, tare da haɓaka ayyuka masu muhimmanci. Waɗannan tsare-tsare ba wai kawai za su haɗa kan al’umma ba ne, har ma za su ƙarfafa kasuwanci, da haɓaka tattalin arziki.

Ganin yadda yanayin fasaha a duniya ke ci gaba da habaka cikin sauri, ƙirƙira, kasuwanci, da kuma samun babban jari sune ginshikai. Wannan bangaren yana zayyana yunƙurin samar da yanayi mai kyau domin ƙirƙira, tallafawa ayyukan kasuwanci tare da jawo zuba hannun jari mai muhimmancin gaske. Idan tafiyar ta bunkasa, tabbas tattalin arzikin dijital na Nijeriya zai ci gaba da kasancewa mai ƙarfi wanda ya zama ruwa abokin tafiya.

Rukuni na karshe, ya yi magana dangane da cinikayya, wanda yake da nufin daukaka matsayin Nijeriya a tsarin fasahar zamani na duniya. Tare da mai da hankali kan kasuwancin fasaha, dabarun haɗin gwiwa, da sabbin tsare-tsare, wannan tsarin na neman ƙarfafa jagorancin Nijeriya wajen ayyana makomar dijital ta Afirka. A yayin da bangaren ICT ke ci gaba da karuwa, kuma aka samun karuwar kashe kudaden kasuwanci ta yanar gizo, wannan bangaren na karshe cikin daftarin tsare-tsaren ministan sadarwa, kirkire da kuma tattalin arzikin dijital, yana shirin kara habaka tattalin arziki.

A yayin kaddamar da wannan tsare-tsare na dabarun bunkasa wannan bangare, Gwamnatin Nijeriya ta bullo da wani yunkuri na kawo sauyi ga Nijeriya. Wannan daftari yana wakiltar alƙawarin kawo ci gaba tare da kira ga duk masu ruwa da tsaki. A yayin da tsarin ya bayyana kuma ya fara daukar saiti, Nijeriya ta dauki hanyar madaidaiciya wajen kawo juyin juya hali a bangaren dijital, kuma a shirye take ta rungumi kalubale da damar dake bangaren a gaba.

Related Posts