Home » Kamfanin Stears ya ɗauki sabon salo wajen faɗaɗa ayyukansa

Kamfanin Stears ya ɗauki sabon salo wajen faɗaɗa ayyukansa

TECH Hausa ya labarta cewa; Stears, wani kamfanin ajiye bayanai da tattara bayanan sirri na Nijeriya, ya ƙaddamar da sabbin ayyuka tare da canza salon kasuwancinsa.

Kamfanin a halin yanzu yana canzawa daga kamfanin dake samar da bayanai ga masu amfani zuwa ga masu huldar kasuwanci.

Stears zai dakatar da fasalin biyan kuɗinsa na mutum ɗaya amma wadanda suke a kan tsarin a halin yanzu za su ci gaba da aiki da shi zuwa lokacin da zai ƙare.

Michael Famoroti, Bode Ogunlana, Abdulrahim, da Preston Ideh sun kafa kamfanin Stears ne a shekarar 2017 domin warware matsalar karancin samun bayanai da kuma nazarin cikakkun bayanai da Nijeriya ke fuskanta.

Tun daga lokacin, Stears ya zama tushen hanyar samun bayanai ga ‘yan Nijeriya tare da zurfaffan bincike da kuma yada su, gami da dandalin sa ido dangane da COVID-19 da kuma bayanan farko na zabukan Nijeriya.

Yvette Dimiri, Daraktan Stears Insights, ya bayyana cewa ra’ayoyin masu amfani da su ya haifar da sauya tsarin kasuwancin na su.

A cikin watan Oktoban 2022, Stears – yana ɗaya daga cikin kamfanuka 60 da Google ta zaɓa a tsarin shirinta na ‘Black Founders Fund’ na shekarar 2022 a cikin Satumban 2022, wanda suka samu karin jarin dala miliyan $3.3 a tashin farko.

A sakamakon hakan ne, kamfanin yake shirin bullo da sabbin hanyoyin samar da mafita dangane da bayanan leƙen asiri, ƙididdiga, ƙimar kasuwa, hasashen yanayi, ƙididdigar ‘yan kasuwa, da manyan bayanan tattalin arziki.

Kamfanin zai ci gaba da buga labarai, wadanda su ne babban jigonsa. Haka kuma yana shirin fadada ayyukansa zuwa kasashen gabashi da yammacin Afirka.

Related Posts