Home » Payday sun tara dala miliyan 3 a Pre-seed

Payday sun tara dala miliyan 3 a Pre-seed

Kamfanin fasahar hada-hadar kudi na Pan-Afrika da ke ba da daman bude asusu ajiya na kasashen duniya (USD, EUR & GBP) ga ‘yan Afirka, ya sanar da tara dala miliyan 3, wanda ya yi niyyar yin amfani da shi don inganta shirinsa na “makomar aiki” ta hanyar hanyoyin biyan kuɗi.

Kamfanin Moniepoint Inc,ne ya  jagoranci zagayen Pre-seed din nasu inda Sauran masu saka hannun jari a zagayen sun hada da Techstars, HoaQ, DFS Lab’s Stellar Africa Fund, Ingressive Capital Fund II, sai kuma sauran Angel investors kamar Dare Okoudjou, shugaban MFS Africa, da Tola Onayemi, shugaban kamfanin Norebase.

Kamfanin Payday sunyi suna a yan kwanakin nan bayan da kamfanin starliks suka zabe su matsayin hanyar biyan kudin starlinks daga Nijeriya,hakan ya daga daraja da kimar Payday sosai.

Shugaban kamfanin Payday

A yanzu da suka samu wannan kudi sunce zasu ci gaba da habaka harkan kasuwan ci tare da fadada yanda suke gudanar da aiyukan su.

Related Posts