Home » Akoi yuwar kaddamar da Jerin Infinix Note 30 a karshen wanan wattan ta mayu 

Akoi yuwar kaddamar da Jerin Infinix Note 30 a karshen wanan wattan ta mayu 

Daga bayanai da muka samu daga majiya me karfi Kaffanin Infinx zai kaddamar da Jerin wayoyin Infinx Note 30, wayar zata zo da sabuwar fasaha wadda kamfin infinix ya kirashi da All-Round FastCharge, fashar zai bai wayar daman caji da igiya har 260W da kuma caji mara igiya 110W (wireless).

All-Round FastCharge ba kawai game da gudun caji  ba ne, har ila yau ya haɗa da fasali kamar cajin bayan fage (bypass)  (dazarn waya ya cika, wayar zata dakatar da battery daga caji da kuma baiwa wayar wuta hakan na nufin zaka iya aiki da wayar akan wutar lantarki kai saye daga caja). Hakanan fasahar tana aiki tare da daidaitattun ka’idojin masana’antu kamar Isar da Wutar ta USB 3.0 kuma tana iya cajin wani wayar (reverse) cajin. Kamfanin infinix sunsa kula gurin yin battery mai dadewa sosai dakuma yanayin zafin waya, hakazali wayar tasan lokacin da ya kamata tayi caji dai dai da lokacin da mai ita yake da bukata.

A baya can, mun ga samfura da yawa suna yawo a shafukan sata zummunta, irin su : Infinix Note 30 Pro, Note 30 VIP da Note 30 5G. Daga wasu  bayanai kuma akoi   vanilla Note 30 (4G) mai  baturin 5,000mAh.  

Related Posts