Home » Paxful sun dawo aiki bayan shafe Sama da wata daya suna rufe 

Paxful sun dawo aiki bayan shafe Sama da wata daya suna rufe 

Paxful daya daga cikin manhajan da ake hada hadar crypto dasu sosai a Nijeriya sun dawo aiki bayan shafe fiye da wata daya da sukayi a rufe.sakamakon barin kamfanin da wasu daga cikin manyan masu kula da kamfanin sukayi.

Ray Youssef shugaban kamfanin na Paxful shine ya fitar da sanarwan dakatar da aiki da sukayi a watan hudu na wanna shekarar, inda yau kuma suka wallafa sanarwa a shafin su na twitter dake nuna sun dawo aiki.

Kamfanin ya mayar da hankali ne kan Afrika, musamman Najeriya, inda yake da masu amfani da manhajar su sama da mutum miliyan daya da rabi 1.5 wadanda suka yi cinikayya na kudin da ya kai dala biliyan daya da rabi 1.5 na cryptocurrencies a kan manhajar paxful tsakanin shekarar 2015 zuwa 2020.

Related Posts