Home » Tecno Camon 20 preimeir 5G

A yau tara (09) ga watan mayu kamfanin tecno ta kaddamar da sabuwar wayar Tecno Camon 20 preimeir 5G wacce take dauke  kira me kew da kuma ingantattun kamarori, battery da kuma memory.

Wayar tazo kamarori masu tsari me kew, 50MP RGBW Babban kemara dake dauke da 23mm f/1.8  glashin hoto tareda sensor-shift OIS. Sannan kuma 108MP 13mm f/2.2 ultrawide kamara dake  dauke da autofocus da yake iya banbance kananu abubuwa da cikin hoto.

Ba iya kamara wayar ta tsaya ba, wayar na dauke da MediaTek Dimensity 8050 chip wadda ya bawa wayar daman aiki da four Cortex-A78 cores da kuma four Cortex-A55 units.

Wayar na dauke da RAM 8GB da kuma  512GB  internal storage.

Daga gaban, wayar tana dauke da 6.67 inch 2400x1080px AMOLED sikirin me dauke da 120Hz refresh rate da kuma fingerprint scanner. 

Daga karshe,  tecno camon 20 preimeir 5G na dauke da battery mai girman 5000mAh wanda ke da saurin chagi har 45W. 

Related Posts