Home » NEMAN KUƊI DA SOCIAL MEDIA

NEMAN KUƊI DA SOCIAL MEDIA


Akwai hanyoyin neman kuɗi a social media da yawa da za mu iya cin moriyada wayoyin hannunmu, wasu rubutu, wasu sauti (audio), wasu hoto mai motsi (video), wasu hotuna da zane-zane (pictures and arts), wasu kuma faɗaɗa kasuwancinsu wajen tallata kayan da suke siyarwa. Dukkan waɗannan “contents” ana wallafa su a wasu social platforms (Facebook, Youtube, Instagram, Tiktok….).
In ka tashi neman kuɗi a social media, ba ya nufi, sha-yanzu magani-yanzu ba ne, a’a, abu na lokaci, wani da wuri, wani sai ya ɗan ja lokaci. Idan ɗora ‘contents’ kake, kana buƙatar ka tara ‘followers’ ko ‘subcribers’. Idan kuma siyar da kaya kake, kana buƙatar aminci da sanuwa, domin mutane za su turo ma kuɗi, su sayi kayan da ba su gani da idanunsu ba a wajenka, saboda aminci.
• TALLACE-TALLACE
A duniyar yau, in kana saida haja (kayan sawa, kayan abinci, magani, ababen hawa, wayar hannu…) ko aiyuka (graphic design, web/app devs, bricklayer, mechanic/electric engineering…) za ka iya amfani da social media wajen talla kayanka ko sana’arka, ma’ana za ka faɗaɗa neman masu siya, daga garin da kake, zuwa jiha, ƙasa dama duniya baki ɗaya, Maryam Gatawa da Abdulhadi Dankama misalai ne a wannan ɓangaren.
Za ka iya amfani a shafinka na Facebook, ko WhatsApp Status, ko profile na Instagram, Twitter ko TikTok, ko ma ka buɗe profile a wurare kamar Jiji.ng – Nigerian Marketplace domin talla, ko LinkedIn domin sanuwa.
Idan kai influencer ne (mai tarin followers), za ka iya karbar tallace-tallace ka ɗora a shafinka na wata manhaja, ko tallata wani mutum a siyasa. Rabiu Biyora ne a wannan ɓangaren.
• RUBUCE-RUBUCE
A da, idan za ka rubutu, ko kana son zama sananne marubuci, akwai buƙatar wallafa basirarka ta rubutu cikin shafin jaridu (columns), ko wallafa littafi (launching). Amma a yau, baka buƙatar ɗaukar lokaci, bin ƙafa, ana ja ma rai… neman a saka rubutunka cikin jarida, ko a taimaka a tara ma jama’a, don a wallafa littafinka.
Idan kana rubutu, baiwar rubutunka ta fito a social media, gidajen jaridu da kansu za suna neman saka wallafarka a shafin jaridarsu. Na biyu, za ka iya bude shafi a Google Blogspot.com, ko WordPress.com, ko buɗe shafi kai tsaye (website). Idan har kana samun kamar 300 visitors a kowacce rana, yawan samun waɗannan traffic zai baka damar dora tallace-tallace (ads). Idan za ka iya samun 100,000 pageviews a wata ɗaya, za su (iya) biyan ka miliyoyin kuɗaɗe.
Haka idan littafi ka rubutu, za ka iya ɗora shi a Amazon.com, ko OkadaBook.com, duk mai bukatar PDFs ko Hardcopy, zai iya siya ta can kai tsaye, ya saka ma kuɗinka a wallet. Nasir I. Mahuta misali ne a wannan ɓangaren.
• KARANTARWA
Masu karantar English, Hausa, Arabic ko French na dama sosai a Social Media ta koyar da ƙa’idojin yare. Haka masu karatun Fasaha, ko Home Management, ko Islamic Studies, Business Management… da sauransu.
Za ka iya bude ONLINE CLASSES, ana biyanka a wata, ko a programme, ka rika koyarwa a Whatsapp, ko Telegram, ko kuma wani shafi da ka bude a yanar gizo.
Misali, a wata, idan ka sa 1k per participant, za ka iya samin 30k – 50k a duk watan duniya. Masu Arewa Computer Library misali ne a nan.
• WALLAFA VIDEO, AUDIO KO HOTO DA ZANE-ZANE
Za kana iya wallafa wani ‘contents’ a social platforms na videos (a Facebook [Reels], Tiktok, Youtube, Instagram, Likee…), ko Audio (a Sportify, iTune, Audiomack, SounCloud…) ko hotouna (a Pinterest, Shutterstock, iStock, Getty Image…) ko zane-zane (a Amazon, Shopify, Etsy…), misali:
• FACEBOOK REELS
In dai za ka iya tara followers sama da 10000 a Reels, a samu an buɗe videos da ka ɗora na sama da 10000 hours cikin ƙasa da wata biyu, Facebook za su baka damar sa ‘ads’ a shafinka. Daga nan, in ka sa video, aka samu an buɗe shi kamar x1000 a cikin wata ɗaya, za a iya biyan ka $35,000 (ka yi converting na wannan kuɗin zuwa NAIRA, ka ga nawa ne).
• YOUTUBE
Idan ka buɗe channel a Youtube, idan za ka iya samun subcribers 1000, kuma aka samu an buɗe videonka na kamar 4000 hours cikin ƙasa da shekara, za su baka damar MONETIZATION, ma’ana, za su baka damar samun kuɗi da Youtube, wajen sanya ads a channels ɗinka.
Idan ka bude tashar Saira Movies, idan kana cikin kallon Labarina, za ka ga a tsakiya suna sa ma talla. A kowanne 1000 views, za su biya ka $9.99 (nawa ne a kuɗin Nigeria?)
• TIKTOK
A Tiktok kuma, ana buƙatar ka tara 10000 followers, da views kamar 100,000 a cikin wata ɗaya. Tiktok na biyan $190 zuwa $360 a kowanne view cikin wata.
• iTUNE, SPORTIFY, AUDIOMACK da GOOGLE PODCAST
A iTune da Sportify, sauti ake ɗorawa (audio), ana biya #1.45 a kowanne ‘streaming’, ana biyan $5 (#2,075) a 1000 streams. A Audiomack, ana biyan $10 (#415) a 5000 streams. A Google Podcast suna biyan #2.2 a kowannen stream… da sauransu.
• WALLAFA ZANE-ZANE DA HOTUNA
Kamar a Alamy.com, bayan ka sami lasisi, idan ka ɗora hoto a wancan shafi, aka sami mai siya (buyer/client), idan wanda ya siya zai hada flier ta talla ce, zai biya $500, idan a cover ta littafi za a yi amfani da shi, za a biya ka $150, idan kuma a online (kamar website, social media…) za a yi amfani da hoton da ka ɗauka ka ɗora a Alamy, za a biya ka $20.
Da kyawawan hotuna da kake ɗorawa a Instagram ko Facebook don neman likes, ka nemi yadda za ka maida kanka BRAND AMBASSADOR, ana amfani da hotunanka wajen tallace-tallace, ana biyanka.
Akwai suran shafuka da ake ɗora zane-zane da hotuna na jeji, ruwa, gine-gine ake siyarwa a sami kuɗi irinsu su Shopify, Amazon, iStock… da sauransu.
Aliyu M. Ahmad
16th Dhul-Hijjah, 1443AH
15th July, 2022CE

Related Posts